THE IMPORTANCE OF TRANSLATION FROM ONE LANGUAGE TO ANOTHER

 THE IMPORTANCE OF TRANSLATION FROM ONE LANGUAGE TO ANOTHER [MUHIMMANCIN YIN FASSARA DAGA WANI YARE ZUWA WANI]

1. Communication ( Harkar Sadarwa). Fassare tana saukakawa a samu sadarwa mai inganci a tsakanin mutane masu mabambantan yararruka. Tana baiwa mutane damar bayyana kansu ko fahimtar wanin su a yaren da suka sani, tana rushe katangu (na bambantar yararruka) ta kara kawo fahintar juna da hadin kai.

2. Education and Learning (Koyarwa da Koyon Ilmi) Fassara tana da gagarumar rawar takawa a harkar koyo ilmi da koyar da shi. Tana taimaka wajen yada ilmai a tsakankanin yararruka mabambanta, dalibai da malamai na ko ina su kai ga nasarar samo ilmai daga ko ina a duniya. Fassarar ayyukan rubuce-rubucen masu koyarwa a cibiyoyin ilmi (academic works), manyan litattafan karatu na koyar da dalibai (textbooks) da su da makaloli na ayyukan bincike-bincike (research papers), abubuwa ne da suke habaka ilmi a tare da kara fadadar sa.

3. Cultural Exchanges (Musayar Al'adu) Fassara ta na kara habaka musayar al'adu ta hanyar saukaka yadda ayyukan adabin baka (literary works), gwanintocin zayyana (art works) da ayyukan hazakar ilmi (intellectual works) na wani wuri su ke iya kara kai wa ga karin wasu dimbin mutanen wuraren na daban. Don haka sai ta ke bayar da dama ga mutane daga jeri da zubin wasu mabambantan al'adu su kai ga fahintar gami da girmama matsayin gagarumar yawaitar gami da bambantakar hanyotin da dan'adam ya ke iya bayyana kan sa (a al'adance).

4. Harkar Kasuwanci Da Saye da Sayarwa (Business and Trade) A wannan zamani na duniyance (globalization), watau yanayin ci gaban zamanin da ya mai da duniya tamkar wani dan karamin kauye karami, yin fassara dole a harkokin kasuwancin zamani harkar saye gami da sayarwa.  Alal misali fassarar nau'ukan bayanai na tallace-tallacen hajoji domin a saya (marketing material), kundayen bayanin da akan hado su da hajojin, domin mai saye ya iya lakantar amfani da su (product descriptions or manuals), fassarar rubutattun yarjejeniyiyin cinikayya (trade contracts), har da fassarorin shafuffukan intanet na masu samar da kayan ko kokarin sassayar da su. Irin wadannan fassarori su kan taimakawa kamfanonin su ci nasarar jajjawo hankulan masaya,  kai wa kasuwannin sassan duniya na kusa ko na nesa  gami da gigginawar hadakokin kasuwanci masu shallake dukkanin iyakoki na bambantar yararruka. Fassara na bayar da dama ga harkokin kasuwanci su fadada izuwa kasuwannin sassan duniya domin su ciyo moriyar su.

5. Diplomasiyya da Alakokin Kasashe (Diplomacy and International Relations) Fassara ta na bayar da matukar dama ta musayar bayanan sakwanni na fahintar juna, a tsakankanin gwamnatocin kasashe, jakadojin kasashe, da kungiyoyi manya da kanana na kasashen. Fassarori masu dikka (accuracy) na tattaunawar jakadu da kasashe, fassarar rubutattun alkawurra da yarjejeniyoyi, fassarar hudubobin shuwaganni, da fassarorin kudurce-kudurce kan abubuwan da aka kai ga cim musu bayan tararruka suna da muhimmanci gagarumi. Su kan taimaka wajen samun hadin kai, warwarewar mishkiloli gami da kara fahintar juna a tsakanin kasashe.

6. Sadarwar Harkar Shari'a da Gudanarwar Mulki ( Legal and Administrative Communication) 

Akwai taimakon da fassara ta ke yi a kokarin da Shari'a take yi natabbatar da ganin cewa kowanne mutum ya kai ga samun cikakkun hakkokin sa duk da bambantar yaren sa ta hanyoyi da dama. Alal misali, fassarar bayanan da ake rubutawa kan yadda shari'a ta ke gudana ( a kotuna), ko na yarjejeniyoyin tsakanin wadanda ake yi wa shari'ar a gaban kotu, ko takardun da akan ciccike na sharudda kan yin hijira daga wannan kasa zuwa waccan, a tare da kundaye na fito da dokokin gwamnatoci (gazettes). Fassarorin dukkanin irin wadannan abubuwan su kan taimakawa mutane su iya yin hijira daga wannan tsari na shari'a ko na gudanarwar mulki izuwa wani a cikin sauki.

7. Harkar Yawon Bude Idanu da Karbar Baki (Tourism and Hospitality)  Fassarar litattafan nusar da matafiyi hanya (travel guide books), kankanan littattafan tallatawar wuraren zuwa da wuraren sauka (brochures), katunan nau'u'ukan abinci da farashin kowanne saki (menus), da takardun otel masu  bayanin abubuwan cikin sa, su kan bai wa bakon matafiyi damar bibbinciko wuraren sauka mafiya dacewa  a gare shi cikin kwanciyar hankali.

8. Kiyayewar Abubuwan Da Magabata Suke Bari (Preservation of Ancestral Heritage) Fassara tana bayar da damar yadda ake iya kiyaye abubuwa masu dama da magabata su kan bari. Fassarar shahararrun litattafan adabin baka, fasahar zance, wake-wake da tatsuniyoyi da hikayoyi ka al'adu da ma rubutattun kundayen tarihi, su suke kara taimakawa a wajen wanzuwar su daga kakanni da iyaye, har su kai ga 'ya'yaye da jikannu. Hakan yana yiwuwa ta hanyar musayar su ta kan iyakokin qasashe a mabambantan yararruka.

Comments

Popular posts from this blog

Mutarjam Enterprises